Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar disko a yayin wani zama na majalisar.
Akpabio yayin zaman majalisar a makon da ya gabata ya faɗawa sanata Akpoti cewa majalisar ba “gidan casu bane” dole ne a bawa mutum izini kafin ya yi magana biyo bayan magana da ta yi ba tare da izini ba.
Maganar da ya yi ta jawo suka daga ƴan Najeriya da dama inda suke ganin tamkar ya ci zarafin sanatan ta hanyar danganta ta da rashin kamun kai.
A yayin zaman majalisar na ranar Talata da ya jagoranta, Akpabio ya bayar da haƙuri inda ya ce da saninsa ba zai wulakanta mace ba kuma ba yayi haka bane dan ya ci zarafin ta.