Lucky Aiyedatiwa ɗantakarar jam’iyar APC a zaɓen gwamnan jihar Ondo shi aka sanar a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar.
Olayemi Akinwumi kwamishinan hukumar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC kuma jami’in tattara sakon zaɓen shi ne ya sanar da haka a ranar Lahadi a Akure babban birnin jihar.
Aiyedatiwa wanda shi ne gwamnan jihar mai ci ya lashe zaɓen a dukkanin ƙananan hukumomi 18 dake jihar da kuri’a 366,781 a yayin da babban abokin hamayyarsa, Agboola Ajayi na jam’iyar PDP ya samu kuri’a 117,845.
Nejo Adeyemi ɗantakarar jam’iyar ADC shi ne yazo na uku a zaɓen da kuri’a 4,138.
Jumillar ƴan takarkaru 17 ne daga jam’iyu daban daban ne suka shiga zaɓen.