Aisha na so ta yi fice a wasan kwallon doki | BBC Hausa

A Najeriya musamman arewacin kasar, sabon abu ne a ga mace na buga wasan kwallon doki.

Amma Aisha Ahmad Suleiman, mai shekara 18 na neman yin fice a wasan kwallon doki.

Ta bayyana cewa ta fara da sha’awar dabbobi musamman dawakai wanda daga baya ta fara wasan kwallon doki.

Ta kuma ce ta fuskanci kalubale daban-daban bayan ta fara wasan kwallon dawaki.

More from this stream

Recomended