
Hakkin mallakar hoto
Twitter/@Sadiya_farouq
Gwamnatin Najeriya ta ce kusan mutum miliyan biyar ne suke son cin moriyar shirin samar da aikin yi ga matasa wanda aka fi sani da N-Power.
Minista a ma’aikatar bayar da agaji da ayyukan gaggawa Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana haka a shafinta na Twitter.
“Kwana 16 ke nan tun da aka bude shafin da ake karbar takardun neman aikin kuma kawo yanzu mun samu takardu miliyan 4.48”, a cewar ministar a sakon da ta wallafa ranar 12 ga watan Yuli.
Ta kara da cewa ita da ma’aikatanta suna aiki tukuru wajen ganin shirin ya tafi kamar yadda ya kamata.
Ranar 26 ga watan Yunin 2020 aka bude shafin neman aikin na N-Power wanda za a dauki mako shida aka karbar takardun neman aikin matasa.
Shirin na N-Power ya fada cikin rudani bayan da a farkon watan nan majalisun tarayya a Najeriya suka dakatar da shirin wanda gwamnatin Æ™asar ta ci alwashin É—aukar ma’aikata masu Æ™aramin Æ™arfi 774,000 har sai sun samu cikakken bayani kan tsarin É—aukar mutanen da za su ci gajiyar shirin.
Matakin ya zo ne kwana guda bayan Æ™aramin ministan kwadago Festus Keyamo ya yi zazzafar jayayya da ‘yan majalisar lokacin da suka nemi ya yi musu bayani yayin wani zama da suka yi da shi a watan jiya.
Sai dai su kansu ‘yan majalisar ana zarginsu da babakere a kan shirin, ko da yake sun musanta.
Shugaban kwamitin kwadago na majalisar wakilai Hon. Muhammad Ali Wudil ya shaida wa BBC cewa damuwarsu ita ce gwamnati ta bijiro da shirin ne don amfanin jama’ar da suke wakilta, don haka suke bibiya don ganin an yi adalci da tabbatar da daidaito.
Haɗin gwiwar majalisar ƙwadagon ya buƙaci sanin hanyar da aka bi aka zaɓo ayarin mutum 20 daga kowacce jiha a Najeriya don yin aikin tantance mutanen da za a ɗauka aikin na wucin gadi.
Ga yadda za ku bi ku yi rijistar Shirin N-Power 2020
A wannan rukuni na C na watan Yunin 2020 masu neman aikin za su yi rijista ne ta intanet a www.npower.fmhds.gov.ng website.
Sannan ba kowa ne zai iya neman aikin ba, sai wadanda shekarunsu ke tsakanin 18 da 35.
Ga abubuwan da kuke bukata a hannun kafin ku nemi aikin:
- Lambar tantance asusun ajiya na banki (BVN)
- Karamin hoto da ake kira fasfo na jpeg ko PNG
- Adireshin i-mail ko lambar wayar wajen aikin
- Sakamakon digiri ko takardar shaidar kammala yi wa kasa hidima
Hakkin mallakar hoto
@ProfOsinbajo
Ko
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar tawagar tattalin arziki
- Ga abin da ake bukatar ku yi da zarar kun shiga shafin intanet din yin rijistar:
- Ku sanya bayanin inda za a same ku (adireshin i-mail da lambar waya) a bangaren da aka ware don yin hakan.
- Bayanan da kuka sanya din zai kai ku cikin i-mail dinku don ku tabbatar da hakan.
- Da zarar kun tabbatar da adireshin i-mail dinku, sai ku cike wajen da aka tanada don sanya lambobi 11 na tantance asusun ajiya na banki (BVN) sannan ku sanya ranar haihuwa ta hanyar farawa da ranar kwanan wata, sai watan haihuwar sa ikuma shekarar haihuwar taku (dd/mm/yr)
- Shafin dan bayani a kanku da kuma na tuntubarku: ku sanya sunan kak, sunanku na yanka da kuma sunan mahaifi, kamar yadda yake a bayanin tantance asusun ajiyarku na banki BVN.
- Shafin bayani kan Ilimi da Shirin: a wannan bangaren za ku sanya matakin iliminku. An bude shirin na N-power ne ga kowa da kowa.
- Shirin N-Tech da N- health kuwa an bude su ne kawai ga masu shaidar kammala digiri.
- Shirin N-Power na bangaren Lafiya na masu digiri da HND da OND ne kamar wadanda suka karanci aikin likita da aikin jinya da Ilimin Tsirrai da Unguwarzoma da Ilimin Sanin Hallayyar dan adam da Ilimin halittun da ido ba ya gani wato Microbiology.
- Kuna bukatar sanya takardar shaidar digirinky a komfuta don aikewa da shi a yayin yin rijistar.
- Shafin bayani kan aikin da aka taba yi da kuma sauran bayanai: Za ku amsa wasu tambayoyi tare da sanya katin shaida. Ga dai katin shaidar da gwamnati ta yarda ku yi amfani da su a kasa:
- Fasfo din tafiye-tafiye
- Katin shaidar zama dan kasa da hukumar NIMC ta bayar
- Ingantaccen lasisin tuka mota
- Katin zabe na dindindin
- Shafin da za ku sake duba bayanan da kyau sannan ku aike
- Ku duba bayanan da kuka cike duka sannan ku aike
- Bayan kun aike za ku samu wata lamba ta musamman, sai ku dauke ta ku adana ta da kyau.
Mutanen da suka cancanci shiga shirin
Hukumomi sun ce shirin zai dauki mutum 400,000 da za su yi aiki a bangarori da dama da suka hada da Noma da lafiya da koyarwa da gine-gine da fasaha
A shekarar 2016 ne gwamnati ta samar da shirin kuma zuwa yanzu an tallafa wa mutum 500,000.