AFCON: Wa zai lashe gasar Masar 2019 – Ahmed Musa, Salah ko Mane?

Kofin Afirka

Za a bayar da dala miliyan 4 da rabi ga duk kasar ta dauki kofin na bana

Za a gudanar da gasar cin kofin nahiyar Afirka da Masar za ta karbi bakunci karo na 32 daga ranar 21 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2019.

A karon farko hukumar kwallon kafar Afirka, CAF, ta amince a 2017 da sauya lokacin da ake yin wasannin daga Janairu zuwa Fabrairu, inda suka koma tsakanin Yuni zuwa Yuli, kuma aka kara yawan kasashen da za su fafata daga 16 zuwa 24.

Tun farko an tsara cewar Kamaru ce za ta karbi bakuncin gasar ta 2019, kuma karo na farko tun 1972, daga baya aka karbe izinin gudanar da wasannin sakamakon rashin ingantaccen shiri da kuma batun Boko Haram da sauran matsaloli.

Tun farko CAF ta tsara cewar za a fara gasar ta bana tsakanin 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli, amma sakamakon Azumin watan Ramadan, hukumar ta mayar da lokacin daga 21 ga Yuni zuwa 21 ga Yuli.

Haka kuma hukumar ta kara ladan kudin da za ta bai wa kasar da ta ci kofin na bana da ma kasashen da suka samu damar buga wasannin.

Filayen da za a yi wasannin

A filaye shida za a gudanar da gasar saboda an samu karin yawan kasashe daga 16 zuwa 24.

Filayen sun hada da Cairo International Stadium da 30 June Stadium a Alkahira da Alexandria Stadium a Alexandria da Suez Stadium a Suez da Ismailia Stadium a Ismailia da kuma Al Salam Stadium da ke Alkahira.

Rukunin da kasashen za su fafata

  • Rukunin A: Masar da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo, Uganda, Zimbabwe
  • Rukunin B: Najeriya da Guinea da Madagascar da kuma Burundi
  • Rukunin C: Senegal da Aljeriya da Kenya da kuma Tanzania
  • Rukunin D: Moroko da Ivory Coast da Afirka ta Kudu da Namibia
  • Rukunin E: Tunisiya da Mali da Mauritaniya da kuma Angola
  • Rukunin F: Kamaru da Ghana da Benin da kuma Guinea-Bissau

Kasashen da za su buga gasar a karon farko

Bayan da aka fadada wasannin daga kasashe 16 zuwa 24 ne hakan ya bai wa wasu sabbin kasashe damar shiga gasar ta bana da suka hada da Burundi da Madagascar da kuma Mauritanyia.

Haka kuma an samu sabbin masu horaswa da za su je gasar a karon farko da suka hada da dan kasar Netherlands, Clarence Seedorf (kocin Kamaru) da dan Mexico, Javier Aguirre (kocin Masar) da kuma dan Burtaniya, Stuart Baxter (kocin Afirka ta Kudu).

‘Yan wasan da ake sa rai za su taka rawargani

1. Sadio Mane


Dan wasan tawagar Senegal mai taka leda a Liverpool
A kakar bana ya lashe kofin Zakarun Turai ya kuma ci kwallo 26 sannan ya taimaka aka zura biyar a raga.

2. Mohamed Salah

Dan wasan tawagar Masar da Liverpool
Mohamed Salah ya ci kyautar takalmin zinare a karo na biyu a jere a gasar Premier, inda ya ci kwallo 22 ya kuma taimaka aka zura 11 a raga a Liverpool a bana.

3. Hakim Ziyech


Dan wasan tawagar Moroko da Ajax

Daya daga fitattun ‘yan kwallon Ajax, Hakim Ziyech, inda ya ci kofi biyu a bana a Netherlands da kuma kai wa karawar daf da karshe a Champions League.

Dan kasar Morokon ya zama dan wasan da ya fi yin fice a Ajax kaka biyu a jere, inda ya ci kwallo 21 ya kuma taimaka aka zura 24 a raga a bana.

4. Odion Ighalo

Dan wasan tawagar Najeria, Odion Ighalo shi ne kan gaba wajen ci wa Super Eagles kwallaye a wasannin neman shiga gasar ta kofin Afirka.

An yi rade-radin cewar Barcelona za ta dauke shi a watan Janairu, bayan da ya taka rawar-gani a Changchun Yatai mai buga gasar Chinese Super League, inda ya ci kwallo 21 a wasa 28 da ya yi a kakar bana.

5. Riyad Mahrez

Riyad Mahrez ya dauki kofin Premier a bana, ya kuma ci kwallo bakwai a wasa 27 da ya buga wa Manchester City.

Tuni dan wasan ya ci kwallo uku a gasar kofin Afirka, inda ya zura wa Senegal daya a 2015 sannan ya daga ragar Zimbabwe sau biyu a 2017.

6. Gana Gueye

Dan wasan da Paris Saint-Germain ke zawarci Idrissa Gana Gueye zai wakilci Senegal a gasar ta bana.

Ya buga wa Everton karawa 33 a bana, ya kuma nuna kwarewar da yake da ita a fagen buga tsakiya a wasannin Premier.

7. Kalidou Koulibaly

Dan wasan Napoli mai tsaron baya Kalidou Koulibaly shi ne ake cewa yana kan gaba wajen tsaron baya, kuma Manchester United na son yin zawarcin dan kwallon mai shekara 27.

Koulibaly ya fara yi wa tawagar Senegal tamaula a 2015, kuma kawo yanzu ya buga wasa 32.

8. Achraf Hakimi

Dan wasan tawagar Moroko Achraf Hakimi ya yi wasa aro a kakar da aka kammala a Borussia Dortmund.

Hakimi ya lashe Champions League a Real Madrid a 2018 ya kuma buga kofin duniya a 2018 da aka yi a Rasha.

9. Nicolas Pepe

Nicolas Pepe ya taimaka wa Lille ta yi ta biyu a gasar Faransa, inda ya ci kwallo 22 ya kuma taimaka aka zura 11 a raga.

Manyan kungiyoyin Turai na son daukar dan wasan tawagar Ivory Coast cikinsu har da Liverpool da kuma Bayern Munich.

10. Wilfred Ndidi

Wilfred Ndidi daya ne daga fitattun matasan ‘yan wasa a gasar Premier a bana, wanda ya buga wa Leicester City dukkan wasanni 38.

Ya buga wa Super Eagles wasa 25 ciki har da guda uku da ta yi a gasar kofin duniya a Rasha a 2018.

Shin ko kuna ganin da wasu ‘yan wasan da za su taka rawar gani a Masar? Ku aiko mana da naku zabin a shafinmu na BBC Hausa Facebook.

More from this stream

Recomended