
An gudanar da wani zaman sulhu da yan bindiga a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina tare da yan bindiga ciki har da gawurtaccen dan bindinga Ado Aleru da hukumomin tsaro su ke nema ruwa a jallo.
Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi ya rawaito cewa a yayin zaman na masu ruwa da tsaki Aleiro ya zayyano wasu matakai da idan aka dauka za su kawo zaman lafiya a tsakanin Fulani da kuma sauran al’ummar dake zaune a yankin.
Shiga sulhun da ya yi na zuwa ne a dai-dai lokacin da jami’an tsaro ke cigaba da kokarin kama shi tare da ruguza rundunarsa biyo bayan hare-hare da yan bindiga suke kai wa a jihar.