Adikon Zamani: Gwagwarmayar ‘yar takara a lokacin zabe

[ad_1]

Wani sabon salo a siyasar Najeriya shi ne na yadda mata masu yawa suka fito neman a zabe su a mukaman siyasa daban-daban da za a yi takararsu a shekarar 2019.

Wannan batu abin faranta rai ne ga yawancin mata, saboda karancin mata a cikin masu rike da madafan iko batu ne da ya dami ‘yan Najeriya da dama.

Amma duka da cewa matan sun fito sosai domin nuna kwarewarsu da cancantarsu, amma ana ganin jam’iyyun siyasa da wasu mazan na kokarin dakile wannan yunkuri na mata ‘yan siyasa.

Da alama an fara samun sauyin ra’ayi game da shigar mata fagen siyasa, amma tambayar ita ce shin suna samun nasarori kuwa?

A wannan makon, muna duba dalilan da suka sa mata ke kokawa duk da cewa al’ummar kasa na mara musu baya.

Shin kana iya zabar mace idan ta tsaya takara?

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...