
Ademola Adeleke,dan takarar jam’iyar PDP a zaben gwamnan jihar Osun na ranar Asabar 16/07/22 shi ne ya samu nasarar lashe zaben kujerar gwamnan jihar.
Adeleke ya kayar da gwamna mai ci Gboyega Oyetola na jam’iyar APC.
Hukuymar zabe ta INEC ta sanar da cewa Adeleke ya samu nasara da kuri’u 403,371 a yayin da gwamna Oyetola na jam’iyar APC ya samu kuri’u 375, 027.
Duk da cewa yan takara sama da 15 ne daga jam’iyu daban-daban suka samu damar shiga zaben fafatawa mai zafi a zaben ta kasance tsakanin yan takara biyu ne.