ABIN MAMAKI: Wata mata ƴar shekara 70 ta haifa tagwaye

Wata mata ‘yar kasar Uganda, Safina Namukwaya, ‘yar shekaru 70, ta haifi wasu tagwaye – namiji da mace, bayan da suka samu juna biyu ta hanyar maganin hadi, kamar yadda BBC ta ruwaito ranar Alhamis.

Namukwaya ta samu nasarar haihuwa ne a ranar Laraba a asibitin mata na kasa da kasa da kuma cibiyar haihuwa da ke Kampala babban birnin Uganda.

Asibitin ya ba da labarin haihuwar ta shafinsa na Facebook ranar Laraba, yana mai cewa, “Yar shekara 70, Safina Namukwaya, tana magana ne daf da haihuwar kyawawan jariranta. Eh ta haifi tagwaye, namiji da mace. Wannan masarar tarihi ce hakika.

“Yayin da muke girmama wannan uwa mai jajircewa da kuma hasashen samun lafiyar tagwayenta, muna gayyatar ku da ku yi murna tare da mu. Wannan labarin ba kawai game da nasarar likita ba ne; nasara ce game da ƙarfi da juriyar ruhin ɗan adam.”

More from this stream

Recomended