
City ta doke United da ci 3-1 – abin da ya sa ta hawa teburin gasar firimiya
Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce Manchester City ta yi galaba ne a kansu saboda yadda suka yi shiri sosai a wasu wasannin sada zumunta biyu da suka buga a makon da ya wuce.
Man City ta koma saman teburin gasar firimiya ne bayan David Silva da Sergio Aguero da kuma Ilkay Gundogan sun zura kwallo daya-daya kowannensu – abin da ya ba su maki uku a filin wasa na Etihad.
A ranar Lahadi ne City ta doke United da ci 3-1, abin da ya sa United din ta tsaya a mataki na takwas a teburin gasar.
Mourinho ya ce City ta samu galabar ce saboda sun doke Southampton da kuma Shakhtar Donetsk a gida inda suka ci kwallaye 12-1 jumulla.
Ya ce wadannan nasarorin sun fi wadda United ta samu tasiri, kafin karawarsu.
Wannan ne wasa na uku a jere ba a gida ba da United ta yi, biyo bayan doke Bournemouth a gida da waje a karshen makon jiya da kuma nasarar da ta samu a kan Juventus a ranar Laraba.