Abin da ya sa kasashen Yammacin Afirka suke kyamar Faransa

  • Daga Paul Melly
  • Mai sharhi kan Afirka
Zanga-zangar kin jinin Fransa a Bamako, Mali - 22 Satumba 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Aan yi ta zanga-zanar kin jinin Faransa a kasar Mali

Lamarin ya fara sannu a hankali. Yaya aka yi lamuran suka dagule? Me ya sa farin jinin Faransa ya dusashe a Afirka?

Shugaban Faransa Emmanuel Macronya kara yawan agajin da ake bai wa yankin, ya fara dawo da kayan tarihin da aka sace wa yankin zamanin mulkin mallaka, ya kuma kara matsa kaimi wajen janyo matasan yankin cikin harkokin da suka shafi nahiyar.

Ya girke dakarun Faransa a yankin Sahel domin yakar mayakan da ke ikirarin jihadi da suka kashe daruruwan farar hula, da ‘yan sanda da sojoji, ya kuma mara wa kungiyar Ecowas baya da kokarin ganin an kare siyasa daga mamayar sojoji.

A bana ya yi balaguro zuwa Rwanda domin bayyana karara gazawar kasarsa a lokacin kisan kare-dangin da aka yi a kasar a shekarar 1994.

Duk da hakan, Faransa ta tsaya wa Afirka a makoshi, korafi ya yi yawa a kanta sannan ana yawan sukar kasar, lamarin da aka dade ba a gani ba.

A watan da ya gabata, tawagar motocin sojojin Faransa da ke kan hanyar zuwa arewaci domin taimakawa a yaki da ‘yan ta’adda, amma masu zanga-zanga suka hana su wucewa tsakanin iyakokin Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.

A watan Satumba an yi ta aikewa Firaiministan Mali Choguel Maïga sakon jaje, lokacin da ya yi jawabin zargin Faransa da watsar da kasarsa a tsaka da yaki, bayan matakin Macron na janye aike dakaru daga kasar.

Ana samun manyan masu sharhi kan lamuran da suka shafi Afirka, da matasa na kiraye-kirayen a kawo karshen amfani da takardar kudin CFA, wadda kasashe rainon Faransa ke amfani da ita. Masu sukar lamarin na ganin a fakaice Faransa na ci gaba da mulkarsu ne, yayin da ita kuma Faransa ke cewa saboda samun daidaiton tattalin arziki ne.

Zamanin mulkin mallaka a fakaice

Me hakan ke nufi? Ta yaya aka yi sabon shugaban Faransa ya damu da Afirka, fiye da wadanda suka gabace shi, da wanyewa da yadda nahiyar ke sauyawa, da kuma ta yaya aka yi farin jinin Faransar bai ragu ba gwamman shekarun da suka gabata?

Masu suka sun ce watakila hakan na faruwa ne saboda girman kan Mista Macron, da nuna dagawa, da yadda yake salon shugabancinsa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
Duk da son gogayya da ‘yan Afirka, farin jinin Macron ya dusashe

Shi ma ya dan yi kura-kuran difilomasiyya.

Bayan mutuwar sojojin Faransa 13 a hadarin da helikwaftan da suke ciki ya yi a kasar Mali, a watan Nuwamba 2019, ya bukaci shugabannin kasashen Afirka ta Yamma su halarci taron gaggawa a Faransa, lamarin da aka yi wa kallon na zamanin mulkin mallaka, musamman yadda Mali da Jamhuriyar Nijar suka fuskanci kalubale a lokacin mutuwar sojojin kasashen.

Sai dai tun kafin zuwan Mista Macron a shekarar 2017 farin jinin Faransa ya fara dusashewa.

“Za a iya alakanta hakan da ce-ce-kucen da aka yi fama da shi lokacin mulkin mallaka. Yawancinmu ‘ya’yan wadanda sun ga zahirin abin da ya faru ne a wancan lokacin, da irin wulakanci da cin zarafin da aka yi,” in ji wani dan siyasa a Ivori Coast mai suna Sylvain Nguessan.

A farko-farkon samun ‘yancin kai, Faransa ta yi kokarin ci gaba da alakar kut-da-kut da nahiyar Afirka da kokarin da fakaicewa da ba ta kariya, amma har a lokacin batun kare hakkin dan adam yana nan ba tare da ana dubawa ba.

Gazawar da ta fito a zahiri ita ce lokaci kisan kare-dangi da aka yi a Rwanda a shekarar 1994, lokacin da Faransa ta gaza yin wani abu a matsayinta na babbar aminiyar kasar, shugaba mai ci Juvenal Habyarimana, ya fara shirin kisan kare-dangi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
Takardar CFA ita ake amfani da ita tun zamanin mulkin mallaka a kasashen da Faransa ta mulka

Daga tsakiyar shekarun 1990, yawancin gwamnatoci sun yi kokarin ganin Faransa ta ci gaba da hulda da Afirka, da kokarin ganin na kafa dimokuradiyya.

Sai dai daga bisani komai ya watse.

Nicolas Sarkozy ya fara mulki a shekarar 2007 da wani salo da ke nuna dan Afirka bai wani shiga cikin tarihi ba. Ya fifita tsofaffin abokan hulda misali iyalan Bongo, wanda ke mulkar kasar Gabon tun shekarar 1967.

A lokacin da François Hollande ya fara shugabanci a shekarar 2012, ba shi da wani zabi face mayar da hankali kan tabbatar da tsaro yankin Sahel. Bai samu lokacin mayar da hankalin yaukaka dangantakar siyasa ba.

Bayan hawan mulkin Mista Macron, ya san cewa Faransa da shugabanta na bukatar kawo sauyi, da sauyin siyasa a kasar.

A shekarar 2017 ya shaida wa dalibai a babban birni Burkina Faso, Ouagadougou, cewa Faransa za ta bayar da muhimmanci wajen yi garanbawul kan kudin CFA idan gwamnatocin Afirka suna bukatar hakan. Ya kuma gayyaci kungiyoyin farar hula, da matasa, da masu yaukaka al’adun gargajiya zuwa wani taron koli.

Tsohon ciwon da ke damun yankin Sahel

Sai dai yadda ya gagara kalubalantar tsohon tsarin da aka bi lokacin mulkin mallaka, ba ya wani tasiri sosai ciki har da wadanda suke ikirarin bukatar a kawo sauyin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
Duk da kokarin Faransa na magance matsalar ta’addanci, myakan jihadi na ci gba da cin karensu a yankin Sahel

Har wa yau, yanayin da ake ciki a yankin Sahel ya kara tabarbarewa tare da tayar da tsohon miki.

Kasancewar sojojin Faransa a yankin ya kara dagula lamura, tare da fusata wasu a Afirka.

Duk da kokarin da ake yi wajen girke sojoji, tare da girke sojoji 5,000 da kisan sama da 50, Faransa ta gagara magance barazanar mayakan jihadi, wadanda ke kai hare-hare ga farar hula da jami’an tsaro.

Dalilan duka na cike da sarkakiya, daga batun sojoji, da na jama’a, da tattalin arziki da na muhalli.

Sai dai jin ta bakin mutane da ka yi kan yadda suke kallon Faransa, da yadda suke ganin kasashen yammacin duniya ya kamata su magance matsalolin, da kuma janyewar su matukar ba za su iya ba.

Wannan na daga cikin abin da ke zaburar da masu zanga-zangar da suka toshewa dakarun Faransa hanya.

Wannan na zuwa sakamakon jin haushin da suke yi tun da fari, kamar yadda Mista Nguessan ya bayyana: “Jawabin da Sarkozy ya yi a Dakar, da wanda Macron ya yi a Ouagadougou; da yaki a Ivory Coast; da karayar da aka yi kan sakamakon yaki da ta’addanci.

“Da tambayoyi kan kudin kasashen, da bashi, da nuna goyon baya ga masu mulkin mulaka’u da kalmomin tunzuri, duka sun taka rawa wajen yamutsa lamura.”

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
A na kallon Faransa har yanzu tsohuwa mai mulkin mallaka, ko da kuwa ta na goyon bayan dimkradiyya

Wani babban jami’in soji a yankin Sahel military, ya ce ya na kallon Faransa a matsayin miniyar tshohon shugaban ‘yan tawaye Buzu a arewacin Mali, zargin da Faransar ta sha musantawa.

Akwai tababada kan rawar da kasar ke takawa a goyon bayan kungiyar Ecowas – wadda a halin yanu ke kokarin matsawa jagororin juyin mulkin kasashen Mali da Guinea, domin dao da kasashen turbar dimukradiyya.

Ana samun karin mutane da matasan Afira da ke kallon ECOWAS ba ta sukar lamitin yadda ake tafiyar da tsarin mulki a yankin, da shugabannin farar hula da ke yi wa mulkin dimukradiyya kisan mummuke, da amincewa gwamnatin soji da ke yi musu romon bakar kawo sauye-sauye masu inganci.

Paul Melly mai sharhi a Chatham House da ke London.

More from this stream

Recomended