Abin da muka sani kan harin kuskure na sojoji a wani kauye a Katsina

Ana ci gaba da kokarin ceton rayukan wasu mutane da ake zargin bam ya auka wa gidajensu a wani samame da mayakan sojin saman Najeriya suka kai wa ‘yan bindiga a yankin karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Sai dai lamarin wanda ya faru ranar Talata da daddare ya bar tambayoyi birjik a zukatan al’umma musamman kan mabambantan bayanai daga mazauna ƙauyen na Kunkunan Bayan Dutse da rundunar sojin kasar.

A yayin da mazauna ƙauyen ke cewa jirgin sojin Najeriya ne ya jefa musu bam a garin neman mafakar ƴan bindiga, ita kuwa rundunar sojin a sanarwar da ta fitar ba ta ambaci jefa bam a kan fararen hula ba, baya ga cewa ta yi nasarar kashe ƴan bindiga.

Bayanai sun ce, akalla mutum 12 suka ji munanan raunuka, aka kuma rasa rai daya.

Aukuwar wannan lamari da kuma yawan hare-haren ‘yan bindiga sun jefa jama’ar yankin cikin zaman dar-dar.

Sai dai rundunar sojan sama ta kasar ta yi ikirari cewa, dakarunta sun halaka ‘yan ta’adda 24 a harin da ta kai yankin.

Karin wasu labaran da za ku so ku karanta

Me mazauna yankin suka ce?

Wannan lamari dai ya rutsa da mutane da dama, wanda Alhaji Muhammad Kabir Umar, shugaban karamar hukumar, ya ce tuni an kai su asibiti.

Ya ce “Jirgin ne ya je garin jefa wa ƴan bindiga bam sai aka kuskure ya jefa wa mutanen garin Kunkuman.

A lokacin da BBC ta zanta da shi ya ce yana ɗakin gaggawa na babban asibitin ƙwararru na tarayya a Katsina tare da marasa lafiya bakwai.

“Mutum 14 ne suka ji raunuka, shida daga ciki an musu magani a asibitin Dusinma, sai kuma takwas daga ciki aka aika mu zuwa asibitin ƙwararru na Katsina.

“Kafin mu fita daga Dutsinman ma ɗaya ya rasu,” a cewar shugaban ƙaramar hukuar Safanan.

Haka kuma BBC ta zanta da wani mutum da abin ya rutsa da gidansa wanda ya bukaci a sakaya a sunansa.

“Da misalin karfe 11, muna zazzaune a waje iyalanmu kuma na cikin gida, kawai sai muka ji jirgi na shagwagi a sama, kan ka ce wannan sai muka ji wani abu ya taho fuuuu, kawai sai muka ji shi ya faɗo cikin gidajenmu.

“Yanzu haka tarkacen abubuwan da suka zube na nan a tare a ƙofar gidajenmu.

Mutumin ya ce da idonsa ya ga kusan mutum 30 da abin ya shafa, yana mai cewa yawan ya fi abin da hukumomi suka faɗa.

Sannan ya ce akwai wata mata da ya sani da ta rasu.

Me rundunar sojin Najeriya ta ce?

A wata sanarwa da runudar sojin saman Najeriyar ta fitar ranar Laraba, ba ta ambaci batun jefa bam a ƙauyen Kunkuna ba, sai bayanin nasarar da ta samu wajen halaka ƴan ta’adda 24.

Rundunar sojin saman Najeriyar ta ce ta samu wannan nasara ce sakamakon wani sintiri da aka shirya bisa kyakkyawan tsari tsakanin mayaƙan sama na rundunar Operatin Hadarin Daji da wasu jami’an ƴan sanda a wasu kauyuka na jihar Katsina a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce wasu mutanen ƙauye sun ba da tabbacin kashe wannan adadi na ƴan bindiga.

Rundononin hadin gwiwar sun yi wannan atisaye ne a ƙauyukan Zakka da Umadan na ƙaramar hukumar Safanan.

“A yayin da ake sintirin saman, an samu bayanan sirrri daga matuƙan jirgin da suka ce sun gano ƴan ta’adda tsakanin ƙauyen Zakka da Umadan.

“Kafin sannan ƴan ta’addan sun kai hari ofishin ƴan sanda na garin Zakka bayan da suka far wa na Dutsinma har suka kashe wani babban jami’in ɗan sanda.

“Daga nan ne jirgin yaƙin sojin ya karkata wajen da abin ya faru tare da nazartar yankin, inda daga ƙarshe aka gano ƴan bidngar a wani ƙauye mai isan kilomita 7.1 daga Safana,” in ji sanarwar.

Ta ƙara cewa sojojin sun ga mutane na guduwa daga ƙauyen a lokacin da ƴan bindigar ke bi gida-gida.

Sannan daga baya aka gano ƴan ta’addar a ɓoye a wani gini kusan kilomita daga kusa da ƙauyen.

“A wannan lokacin ne aka bayar da izinin buɗe wuta daga sama.

“Sannan kuma jirgin yaƙi ya ci gaba da lugude a wajen a kan ƴan ta’addan.”

A ƙarshe rundunar sojin ta ce an ga mutanen ƙauyukan na komawa matsugunansu bayan kammala samamen.

More News

An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo,...

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...