Abdulsamad ya bada gudunmawar naira biliyan 2 domin sake gina masallacin Juma’a na Zazzau

Sama da naira biliyan 3 aka tara a wurin taron gidauniyar sake gina masallacin Juma’a na masarautar Zazzau.

Gudunmawa mafi tsoka ta fito ne daga hannun mai kaddamarwa kuma shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabiu wanda ya bayar da naira biliyan biyu.

Mataimakin mai kaddamarwa, Alhaji Dahiru Barau Mangal ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 shima Mista Wale Tinubu ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 a yayin da shima Alhaji Musa Bello ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100.

Alhaji Yahaya Bello, Alhaji Kassim Bukar, Alhaji Aliyu Dikko da Alhaji Sulaiman Barau kowannensu ya bayar da gudunmawar naira miliyan 50.

Taron gidauniyar samar da kudin sake gina masallaci ya gida ne a cibiyar taro ta Shehu Musa Yaradua dake Abuja da yammacin ranar Asabar.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon É—an majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...