Abbas ya janye dokar tilastawa yan Najeriya yin zabe

Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya janye kudirin dokar dake neman hukunta duk mutumin da ya cancanta  ya yi zabe amma  ya ki yi.

Abbas da kuma Daniel Ago dan majalisar dake wakiltar mazabar Bassa/Jos North ta jihar Plateau a majalisar ne suka gabatar da kudirin a gaban majalisar wakilan.

A ranar 15 ga watan Mayu ne dokar ta tsallake karatu na biyu a majalisar.

Da yake jagorantar tattaunawa kan kudirin Agbo ya ce dokar na neman gyara dokar zabe ta 2022 domin magance matsalar rashin fitowar masu kada kuri’a.

Dokar ta bukaci a daure mutum tsawon watanni shida ko kuma tarar N100,000 ga wadanda suka cancanci kada kuri’a amma su ka ki zuwa yin zabe.

Amma kudirin ya samu suka daga yan Najeriya da su ka fito daga bangarori da dama da suka hada kungiyoyin fararen hula da kuma Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya NBA.

Kungiyar ta NBA ta ce dokar cibaya ne kuma ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, Musa Krishi  mai taimakawa shugaban majalisar kan kafafen yada labarai ya ce Abbas ya janye kudirin ne domin bayar da damar tattaunawa da masu ruwa da tsaki da suka fito daga bangarori da dama.

More from this stream

Recomended