Abba Gida-gida ya fara ba da tallafin karatun naira 20,000 ga ƴara mata dubu 45 a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta fara bayar da tallafin Naira 20,000 ga ‘yan mata 45,000 domin tallafa wa ilimin ‘ya’ya mata tare da karfafa gwiwar iyaye su tura ‘ya’yansu mata zuwa makaranta.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wajen bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun ‘yancin kai wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Ya ce, “domin tallafa wa ilimin ‘ya’ya mata da kuma kwadaitar da iyaye su tura ‘ya’yansu mata zuwa makaranta, muna ba da tallafin Naira 20,000 ga yara mata sama da 45,000 a matsayin shirin gwaji don tallafa musu su ci gaba da karatu.

“Har ila yau, muna sake shigar da motocin bas na yara ‘yan mata don jigilar makarantarsu.”

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa tana kuma gina sabbin makarantu a faɗin kananan hukumomi 44 a kokarin da suke na yi wa duk yaran da ba sa zuwa makaranta da ke yawo a kan tituna.

Hakazalika, ya nanata ajandarsa ta tallafawa a manyan matakai ta hanyar tura dalibai 1001 da suka kammala karatun digiri na farko da sakamako na matakin farko don yin digiri na biyu a jami’o’in kasashen waje.

More News

Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar...

Ƴansanda a Katsina sun yi nasarar cafke wasu tantiran masu safarar alburusai wa ƴanbindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

Mutanen Isra’ila sama da rabin miliyan sun tsere saboda yakin Gaza

Mutanen Isra'ila sama da rabin miliyan ɗaya ne suka fice daga ƙasar kuma ba su koma ba a watanni shida na farkon yaƙin Isra'ila...