Kungiyar kwadagon Najeriya ta dakatar da yajin aikin gama garin da take yi don menan karin albahi.
Shugaban kungiyar Ayuba Wabba ne ya sanar da dakatar da yajin aikin a wani taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi.
Ya ce dakatar da yajin aikin ya fara aiki ne daga ranar Lahadin.
Sai dai kuma ma’aiakta da dama ba za su yi aiki ranar Litinin ba domin hutun bikin samun ‘yancin kan Najeriya.
Kungiyar kwadagon tana neman a kara wa ma’aikata albashi ne daga mafi karancin albashin naira 18,000 zuwa kimanin naira 50,000.
Shugaban kungiyar kwadagon ya bukaci gwamnatin kasar ta dawo da kwamitin tattaunawa.
Sannan ministan kwadagon Najeriya, Chris Ngige ya tabbatar da cewa gwamnati za ta dawo da kwamitin tattaunawa tare da yin la’akari da bukatun kungiyar a ganawar da za su yi nan gaba.