Ministan harkokin sadarwa, Adebayo Shittu ya maka jam’iyar APC kara gaban kotu bayan da jam’iyar ta ce bai cancanci tsayawa takaraba a karkashin ta.
Shittu ya nemi tsayawa takarar, gwamnan jihar Oyo a karkashin jam’iyar APC.
Kwamitin tantance yan takara na jam’iyar ya cire Shittu daga cikin yan takara bayan da ya gaza gabatar da shedar kammala hidimar kasa wato NYSC.
A cewar kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, a ƙarar da Shittu ya shigar ya kalubalanci cewa ba dai-dai bane jam’iyar ta cire sunansa daga yan takara saboda kin halartar NYSC.