Sanata Abdul Ahmed Ningi, mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, ya nuna damuwa kan hare-haren saman da Amurka ta kai kan wuraren ‘yan ta’adda a Jihar Sokoto ba tare da neman izini ko tuntuɓar Majalisar Dokokin Tarayya ba.
Sanatan ya bayyana hakan ne a zauren Majalisar Dattawa, inda ya ce matakin ya saɓa wa ikon ƙasar tare da karya tsarin sa ido na majalisa kan harkokin tsaro.
Ya ce, “hakan ya saɓa wa ikon ƙasar tare da karya tsarin sa ido na majalisa kan al’amuran tsaro.”
Sanata Ningi ya ƙara da cewa Majalisar Dokoki na da rawar da doka ta tanada a harkokin tsaro da shigar sojojin ƙasashen waje, amma ba a nemi ra’ayinta ba kafin kai harin.
A cewarsa, “majalisar dokoki na da rawar da doka ta tanada a harkokin tsaro da kuma shigar sojojin ƙasashen waje, amma ba a nemi ra’ayinta ba kafin kai harin.”
Ya kuma gargaɗi cewa barin ɓangaren zartarwa ya yanke irin wannan hukunci shi kaɗai na iya haifar da matsala nan gaba.
Sanatan ya ce, “barin ɓangaren zartarwa ya yanke irin wannan hukunci shi kaɗai na iya buɗe ƙofa ga wasu ƙasashe su ma su ɗauki mataki makamancin haka nan gaba.”
Biyo bayan wannan batu, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da cewa Majalisar za ta gudanar da zama domin tattaunawa da ‘yan majalisa kan lamarin.
Ya ce an shirya yin bayanin tun da farko, amma aka ɗage shi domin girmama marigayi Sanata Godiya Akwashiki.
Sanata Ningi Ya Soki Harin Sama Da Amurka Ta Kai A Sokoto Ba Tare Da Izinin Majalisa Ba

