’Yan Sanda A Kano Sun Kama Matashi Mai Shekara 25 Kan Cin Zarafin Mahaifiyarsa, Sun Kuma Kwato Bindiga A Hannunsa

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da cafke wani matashi mai shekara 25, Ididiong James, bisa zargin dukan mahaifiyarsa tare da mallakar bindigar Beretta ta Ingila da harsasai takwas.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Laraba, ya ce jami’an ’yan sanda na sashen Panshekara sun kai dauki a ranar 25 ga Janairu bayan samun kiran gaggawa kan abin da ake zargin matashin na aikatawa.

Sanarwar ta ce jami’an sun tarar da matashin yana “bugun mahaifiyarsa ba tare da tausayi ba a gidansu da ke Unguwar Panshekara, Kano.”

Ta kara da cewa wanda ake zargin ya tsere da zuwan ’yan sanda, amma mahaifiyarsa ta mika bindigar da harsasai. Ta bayyana cewa ta gano su a cikin jakar danta, ta kuma ki mayar masa da su.

Har ila yau, ta nuna damuwa kan sauyin halayen danta tun bayan dawowarsa daga bikin Sabuwar Shekara.

Sanarwar ta ce daga bisani an kama wanda ake zargin, kuma yana tsare a hannun ’yan sanda. Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya yabawa mahaifiyar kan jarumta, tare da yin kira ga iyaye da su kasance masu sa ido kan ’ya’yansu.

More from this stream

Recomended