Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar ’yan sanda uku bayan wani hari da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai musu a Ƙaramar Hukumar Bakori.
Mai magana da yawun rundunar, Aliyu Abubakar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Katsina.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 12:44 na rana, lokacin da wasu ’yan sanda ke gudanar da sintiri na yau da kullum domin dakile aikata laifuka a hanyar Guga zuwa Bakori.
A cewarsa, ’yan bindigar sun yi wa jami’an kwanton bauna tare da buɗe musu wuta, inda ’yan sandan suka maida martani tare da fatattakar maharan.
Aliyu Abubakar ya ce ’yan sanda uku sun rasa rayukansu sakamakon harbin bindiga, yayin da wasu biyu suka samu raunuka.
Ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa wani asibiti mafi kusa, inda ake ci gaba da ba su kulawar lafiya.
Rundunar ’yan sandan ta ce ta fara bincike domin gano tare da cafke waɗanda suka kai harin.
Ƴan Bindiga Sun Kashe ’Yan Sanda Uku A Wani Harin Kwanton Bauna A Katsina

