Hukumomin Tsaro Sun Samu Jami’an Soji 16 Da Laifin Yunkurin Juyin Mulki

Hukumomin tsaron Najeriya sun bayyana cewa sun samu wasu jami’an soji da laifin yunkurin kifar da gwamnati a shekarar da ta gabata.

Wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasa ta fitar ta ce bincike ya tabbatar da laifin wasu ƙananan hafsoshi 16, waɗanda ake zargi da shirya yunkurin juyin mulki a watan Oktoban 2025 domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rundunar sojin ƙasar ta ce an kama jami’an ne a watan Oktoban bayan zarginsu da rashin ladabi da kuma saɓa wa dokokin aikin soji, lamarin da ya sa aka tsare su tare da buɗe bincike a kansu.

Sanarwar ta ƙara da cewa binciken ya kammala, inda wasu daga cikin sojojin da aka tsare suka amince da shirin yunkurin juyin mulkin, abin da rundunar ta ce ya saɓa wa ƙa’idojin aikin soji da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya.

Shalkwatar tsaron ƙasa ta ce nan gaba za a gurfanar da jami’an gaban kotun soji domin yanke musu hukunci.

A baya-bayan nan, ana yawan jin zarge-zargen yunkurin juyin mulki a Najeriya sakamakon matsalolin tsaro da matsin rayuwa, zarge-zargen da rundunar sojin ƙasar ta sha musantawa.

Najeriya ta taɓa fuskantar juyin mulki da dama tun bayan samun ’yancin kai, musamman tsakanin shekarun 1966 zuwa 1993. Sai dai tun bayan dawowar mulkin dimokraɗiyya a 1999, sojojin ƙasar ke ɗaukar duk wani batun yunkurin juyin mulki da matuƙar muhimmanci.

More from this stream

Recomended