Jam’iyyar APC Ta Karyata Jita-Jitar Sauya Shettima A Matsayin Mataimakin Shugaban Kasa Gabanin Zaben 2027



Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai da ke cewa ana shirin sauya Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaben shekarar 2027.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Felix Morka, ya sanya wa hannu.

A cewar APC, ta lura da karuwar hasashe da jita-jita a kafafen yada labarai kan batun, inda a baya-bayan nan aka fara danganta sunayen wasu mutane da ake zargin za su maye gurbin Mataimakin Shugaban Kasa.

Sai dai jam’iyyar ta jaddada cewa rahotannin ba su da tushe, ba gaskiya ba ne, kuma jita-jita ne kawai. Ta bukaci kafafen yada labarai da su guji yada labaran da ba su da inganci ko dogaro da majiyoyi marasa tushe.

APC ta kuma tunatar da jama’a cewa har yanzu dokoki da ka’idojin zabe sun hana fara harkokin siyasa, inda ta ce tattaunawa kan zaben 2027 a wannan lokaci ba ta dace ba.

Sanarwar ta kara da cewa abin da ya fi daukar hankalin jam’iyyar a halin yanzu shi ne tallafa wa Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima wajen aiwatar da ajandar Renewed Hope, musamman gyare-gyaren tattalin arziki da ke da nufin bunkasa kasa da inganta rayuwar al’umma.

Haka kuma, jam’iyyar ta gargadi ministoci, manyan jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyya da su guji furuci ko matakai da za su iya kara rura wutar jita-jita, tare da mayar da hankali kan aiki tukuru da nuna nasarorin gwamnatin Tinubu.

More from this stream

Recomended