Gwamnatin Kano Ta Gargadi Magoya Bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf Kan Cin Zarafin Kwankwaso

Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da su daina yin kalaman batanci ko tayar da hankali kan jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Daraktan Janar na Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a a Fadar Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayar da gargadin a ranar Asabar yayin rabon babura ga ’yan jam’iyya a dandalin Open Space Theatre da ke Government House, Kano. Gwamna Yusuf ya halarci taron.

Bature ya ce gwamnati ba za ta amince da rashin ladabi ko raini da ake yi wa Kwankwaso ba, yana mai jaddada cewa gudunmawarsa ga siyasar Kano har yanzu tana da muhimmanci duk da sauye-sauyen siyasa da suka faru a baya-bayan nan.

Ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana cin zarafin jagoran Kwankwasiyya zai fuskanci hukunci, yana mai cewa irin hakan ba za a lamunta shi ba.

Kakakin gwamnatin ya bukaci magoya bayan gwamnan da su nuna hakuri da balagar siyasa, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar tashin hankali sakamakon sauya sheƙa da rikice-rikicen siyasa a jihar.

Ya kara da cewa gwamnatin Yusuf na mayar da hankali ne kan tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin magoya bayanta, tare da gargadin cewa sabanin siyasa bai kamata ya rikide zuwa cin mutuncin juna ba.

Bature ya kuma tunatar da ’yan jam’iyya cewa girmama shugabanci da kiyaye da’a a cikin gida na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da kwanciyar hankali da kyakkyawan shugabanci.

More from this stream

Recomended