
Mutane 11 ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a garin Okhuahe dake kan babbar hanyar Benin zuwa Agbor a jihar Edo.
A yayin da wasu bakwai suka jikkata a hatsarin motar da ya faru a ranar Asabar.
Shedun gani da ido sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne lokacin da wata mota kirar Toyota mai cin mutane 18 ta yi gangancin wuce wata mota abin da ya kai ta ga yin tawo mu gama da wata motar dake tawowa.
Kwamandan shiyar Edo na Hukumar Kiyaye Afkuwar Haɗura ta Ƙasa FRSC, Cyril Matthew ya tabbatar da faruwar hatsarin.
Ya ce hatsarin ya rutsa da motar kirar hayis bas da kuma babbar mota.
Matthew ya ce mutane 11 sun mutu nan take a wurin da hatsarin ya faru a yayin da aka garzaya da wadanda suka jikkata ya zuwa asibiti.

