
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a fadar Aso Rock dake Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa anga gwamnan sanye da shigarsa ta farar babbar riga da kuma jar hula ta Kwankwasiya a lokacin da yake shiga ofishin shugaban kasa da karfe 04:13 na yammacin ranar Litinin.
Wannan ne karo na farko da gwamna Yusuf ke ganawa da shugaban kasar tun bayan da Tinubu ya dawo daga birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ganawar na zuwa ne dai-dai lokacin da rahotanni ke cewa gwamnan na shirye-shiryen ficewa daga jam’iyarsa ta NNPP inda zai koma jam’iyyar APC inda ake cigaba da samun tsaiko na kammala shirye-shiryen shigar tasa jam’iyyar ta APC.
Kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga ɓangarorin biyu da aka fitar kan abun da ganawar ta su ta mayar da hankali kai.
Wata majiya dake da masaniya kan batun ta bayyana cewa an samun jinkirin shigar gwamnan jam’iyar ta APC bayan da shuagabancin jam’iyar ya gaza bashi tabbacin cewa za a bashi tikitin takarar kujerar gwamna zaɓen shekarar 2027.

