
Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun kama tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami.
An kama Malami ne a gaban gidan gyaran hali na Kuje dake Abuja a ranar Litinin.
Wani fefan bidiyo da aka watsa a kafafen soshiyal midiya ya nuna tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya yana shiga cikin wata mota mallakin hukumar ta DSS jim kaÉ—an bayan fitowarsa daga gidan yarin.
Kafin ya shiga cikin motar Malami ya nemi jami’an na DSS su nuna masa katin shedarsu ta aiki da kuma wanda yake jagorantarsu.
Wata majiya dake tare da jami’an tsaron ta tabbatarwa da jaridar The Cable cewa an kama Malami.
“Eh gaskiya ne jami’an DSS sun kama Abubakar Malami. Akwai korafe-korafe da dama akansa da suka shafi zargin É—aukar nauyin ta’addanci,”a cewar majiyar.

