Bom da aka dasa akan titi ya jikkata mutane biyar a Zamfara

Mutane 5 ne suka jikkata a ranar Alhamis bayan da wani bom da aka dasa ya tashi akan hanyar Takalafiya-Gadar Zaima dake karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi ya wallafa cewa fashewar bom din ta faru ne lokacin da wani babur dake É—auke da mutane biyar ya bi ta kan bom din da ake zargin yan fashin daji ne suka dana shi domin ya tashi da jami’an tsaro dake yawan sintiri a yankin.

Tashin bom din ya haifar da fashewa mai ƙarfi da ta ragargaza babur din tare da jiwa mutanen dake kai munanan raunuka.

Jami’an tsaro sun yi gaggawar killace titin inda suka hana ababen hawa wucewa tare da shawartar mazauna wurin da su kaucewa zuwa wajejen wurin da abun ya faru ya yin da suke duba ko akwai wani abun fashewar.

An garzaya da mutanen da abun yanshafa ya zuwa asibitin Gummi.

More from this stream

Recomended