Wata babbar kotun jihar Rivers ta bayar da umarnin wucin-gadi na dakatar da yunƙurin tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, Ngozi Nma-Odu.
A hukuncin da ta yanke a birnin Fatakwal, kotun ta umarci kakakin majalisar dokokin jihar, Martin Amaewhule, da sauran waɗanda ake ƙara, ciki har da akawun majalisar da alƙalin alkalan jihar, da su dakatar da duk wani mataki da ya shafi tsige gwamnan, kamar yadda tashar talabijin ta Channels ta ruwaito.
Haka kuma kotun ta bayar da wani keɓantaccen umarni da ya hana alƙalin alkalan jihar, Mai Shari’a Simeon Chibuzor-Amadi, karɓar ƙorafi, miƙa shi, ko duba wata buƙata da ta shafi batun tsige gwamnan daga majalisar dokokin jihar, har na tsawon kwana bakwai.
Gwamna Fubara da mataimakiyarsa ne suka shigar da ƙorafe-ƙorafe daban-daban a gaban kotun, suna neman wannan kariya ta doka.
Jihar Rivers dai na fama da rikicin siyasa tun bayan zaɓen shekarar 2023, lamarin da ya kai ga Shugaba Bola Tinubu dakatar da gwamnan na tsawon wata shida a bara.
Kotun Rivers Ta Dakatar Da Yunƙurin Tsige Gwamna Fubara

