Khamenei Ya Zargi Trump Da Alhakin Mutuwar Masu Zanga-Zanga A Iran

Jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce Shugaban Amurka, Donald Trump, ne ya haddasa mutuwar masu zanga-zangar da suka ɓarke a ƙasar Iran a kwanakin baya.

Ayatollah Khamenei ya bayyana cewa Iran na kallon Trump a matsayin babban mai laifi, yana mai zarginsa da sanya baki cikin rikicin da ya janyo tashin hankali.

Ya kuma zargi wasu mutane da ke da alaƙa da Isra’ila da Amurka da hannu wajen kashe dubban fararen hula da jami’an tsaro a lokacin rikicin.

Jagoran addinin ya jaddada cewa babu wanda zai iya tilasta wa Iran shiga yaƙi, amma ya ce dole ne masu laifi na cikin gida da na ƙetare su fuskanci hukunci bisa ayyukansu.

More from this stream

Recomended