Wani sabon binciken lafiya ya gano cewa babu wata alaƙa tsakanin shan maganin zazzaɓi na Paracetamol ga mata masu juna biyu da haihuwar jarirai masu lalurar galahanga (autism) ko wata nakasasa.
Masu binciken sun bayyana cewa sakamakon binciken ya saɓa da iƙirarin da tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi a bara, inda ya gargadi mata masu juna biyu da su guji shan maganin.
Binciken ya haɗa da nazari mai zurfi kan dubban mata masu juna biyu a sassan Amurka, domin tantance tasirin maganin ga lafiyar jarirai.
Masu binciken sun ce ya dace a kwantar wa mata masu juna biyu hankali cewa za su iya shan Paracetamol idan buƙata ta taso.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa Ma’aikatar Lafiya ta Amurka ta yi watsi da sakamakon wannan bincike.
Bincike Ya Karyata Alaƙar Paracetamol Da Lalurar Galahanga Ga Jarirai

