Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa dole ne ’yan Najeriya su tashi tsaye su haɗa kai domin dakile ’yan ta’adda, ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka da ke addabar ƙasar.
Shehu Sani ya faɗi hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin bikin ƙaddamar da littattafansa guda biyu, The Councillor da The Perilous Path to Europe. Ya ce ba wata ƙasa ta waje da za ta zo ta kuɓutar da Najeriya daga wannan matsala, yana mai jaddada cewa idan jama’a suka haɗa kai, suka waye, tare da samun goyon bayan hukumomin gwamnati, za su iya doke masu tayar da ƙayar baya.
A cewarsa, wasu na ganin kamar su ne masu mallakar ƙasa kuma za su iya tilasta wa kowa ta hanyar amfani da makamai, amma haɗin kai da ƙarfafa guiwar jama’a na iya kawo ƙarshen wannan tunani.
Shehu Sani Ya Ce ’Yan Najeriya Su Tashi Tsaye Domin Dakile ’Yan Bindiga

