Hukumomin shari’a a Burkina Faso sun fara gudanar da bincike kan mutuwar wata tsohuwar ministar gwamnati, bayan da aka tsinci gawarta a gidanta da ke birnin Ouagadougou.
Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa alamun farko sun nuna yiwuwar an kai mata hari kafin rasuwarta.
An gano gawar Yolande ne a ranar Asabar a gidanta da ke unguwar Karpala.
Babban mai gabatar da ƙara, Lafiama Prosper Thombiano, ya bayyana cewa an ɗauki lamarin a matsayin gaggawa. Ya ce an tura jami’an tsaro tare da ƙwararrun masana binciken gawarwaki domin gano yadda lamarin ya faru da kuma gano waɗanda ke da hannu.
Hukumomi sun buƙaci jama’a da su bayar da bayanan da za su taimaka wajen saurin kammala binciken.
Marigayiyar ta kasance fitacciyar ’yar siyasa a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar, Blaise Compaoré, wanda ya shugabanci Burkina Faso na tsawon shekaru 27 kafin kifar da shi a juyin-juya-halin shekarar 2014.
An Fara Bincike Kan Mutuwar Tsohuwar Minista A Burkina Faso

