Gwamnatin Kebbi Ta Sake Buɗe Makarantar Sakandaren Yan  Mata ta Maga

Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da sake buɗe Makarantar Sakandaren Yan Mata dake Maga watanni bayan da aka yi garkuwa da wasu ɗaliban makarantar su 24.

An rufe makarantar ne a cikin watan Nuwamba bayan sace ɗaliban makarantar wadanda jami’an tsaro suka kubutar daga bisani bayan sun shafe kwanaki a hannun masu garkuwar.

Da take magana a wurin taron manema labarai ranar Talata a birnin Kebbi bayan ganawar da ta yi da shugabannin makarantun sakanadare na jihar ,kwamishiniyar ilimi a matakin farko da kuma sakandare, Halima Muhammad Bande ta ce gwamnati ta gamsu cewa makarantar bata fuskantar barazana za a iya bude ta bayan an dauki lokaci ana kula da daliban da abun ya shafa da iyayensu ta hanyar basu shawarwari tare da kuma girke jami’an tsaro domin kara musu kwarin gwiwa.

Bande ta ce gwamnan jihar Nasiru Idris ya bayar da umarnin daukar duk wani matakin tsaro da ya kamata domin kare malamai da dalibai a dukkanin makarantun dake faɗin jihar.

Ta ce gwamnan ya kuma amince da kaddamar da shirin koyawa  shugabannin makarantun dabarun tsaro domin kare faruwar kamancin haka anan gaba.
.

More from this stream

Recomended