
Kungiyar NARD ta likitoci masu neman kwarewa ta janye yajin aikin da ta yi shirin fara yi a ranar Litinin 12 ga watan Janairu.
Kungiyar ta sanar da janye batun shiga yajin aikin ne a cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar Shuaibu Ibrahim ya fitar a ranar Lahadi.
Tun da farko kungiyar ta sanar da shirin shiga yajin aikin ne a ranar 2 ga watan Janairu biyo bayan taron shugabannin kungiyar na kasa da suka gudanar.
A ranar 9 ga watan Janairu ne kotun ma’aikata dake Abuja ta bayar da wani umarnin wucin gadi da ya hana yan kungiyar shiga kowane irin yajin aiki bayan da babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a,Lateef Fagbemi ya shigar da kara gaban kotun.
Amma kuma a sanarwar dakatar da shiga yajin aikin, Ibrahim ya ce an dauki matakin ne biyo bayan taron shugabannin kungiyar da aka gudanar ranar Lahadi, 11 ga watan Janairu.
Ya ce a yayin taron kungiyar ta duba halin da ake cikin kan buƙatun da suke so a biya musu inda suka lura cewa an samu karin fahimta da cigaba a tattaunawar da suke da masu ruwa da tsaki.
Ya ce bayan samun tabbaci daga masu ruwa da tsakin da kuma shigar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima an janye yajin aikin da aka shirya farawa.

