
Wata gobara ta kone ginin sakatariyar ƙaramar hukumar Wukari dake jihar Taraba inda ta lalata ofisoshi, kayayyakin aiki da kuma muhimman takaradu.
Gobarar ta kama ne a ranar Juma’a da misalin karfe 4:30 a sakatariyar dake da nisan kilomita 320 daga Jalingo babban birnin jihar.
Har kawo yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.
Rahotanni sun bayyana cewa an gaza shawo kan gobarar da wuri abun da ya jawo lalacewar yawancin ginin dake cikin sakatariyar ginin ofishin shugaban ƙaramar hukumar ne kaɗai wanda ke tsakiyar harabar sakatariyar ya tsira daga wutar gobarar.
Mutanen yankin sun alakanta girman barnar da gobarar ta yi da rashin ingantattun kayayyakin kashe gobara a karamar hukumar.

