Kotu ta bayar da belin Abubakar Malami, matarsa da ɗansa

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta saka ranar 17 ga watan Fabrairu domin gudanar da shari’ar tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami da kuma wasu mutane biyu da ake zargi da almundahanar kudade.

Har ila yau alkalin kotun mai shari’a, Emeka Nwite ya bayar da belin Malami da ɗansa Abdulaziz da kuma matarsa, Asabe Bashir kan kudi naira miliyan ₦500 kowannensu da kuma mutanen da za su tsaya musu.

Mai shari’a Nwite ya ce  dole ne mutanen da za su tsaya musu su zama suna da kadara a unguwar, Maitama,Gwarinpa ko Maitama dukkansu a birnin tarayya Abuja.

Alkalin ya umarci, Malami da ya mikawa kotun fasfonsa na tafiye-tafiye kuma kada ya sake ya bar kasar nan ba tare da izinin kotun ba.

Har ila yau alkalin ya kuma bayar da umarnin a cigaba da tsare Malami da sauran waɗanda ake kara a gidan yarin Kuje har sai sun cika sharudan belin.

More from this stream

Recomended