Yan bindiga sun yi garkuwa da shararren dan jarida a Kaduna

Yan bindiga sun yi garkuwa da Umar Iyale wani shahararren dan jarida daga gidansa dake Danhonu II dake Kaduna Millennium City.

Iyale wanda yake kwance yana jinyar wani ciwo da ba a bayyana ba an yi garkuwa da shi da misalin karfe 09:00 na daren ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa shi kadai ne a gida lokacin da lamarin ya faru.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni rundunar ta fara ƙoƙarin kubutar da shi.

“Kwamishinan yan sanda na jiha, CP Rabiu Muhammad ya tura wata tawagar jami’an tsaro da za su bi diddigin masu garkuwar tare da ceto Iyale lami lafiya,” ya ce.

Iyale tsohon ma’aikacin gidan talabijin na Æ™asa NTA ne  da kuma gidan talabijin mai zaman kansa na AIT a jihar Kaduna kuma ya yi ritaya yan  shekarun baya da suka wuce.

More from this stream

Recomended