Rundunar tsaro ta Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) reshen jihar Kano ta sanar da kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu wajen kisan wani jami’inta, AbduRauf A. Shariff, yayin da yake kokarin hana aikata laifi.
Mai magana da yawun rundunar a jihar Kano, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana cewa marigayin, mai shekaru 29, yana bakin aiki ne a tashar Court Road lokacin da aka kai masa hari.
A cewarsa, wasu bata-gari ne suka taru dauke da makamai suna aikata satar waya da wasu laifuka, lokacin da jami’in ya yi kokarin dakatar da su. Sai dai, maharan sun yi amfani da makamai suka jikkata shi matuka, daga bisani suka kashe shi.
SC Abdullahi ya ce jami’an tsaro da suka isa wurin sun samu nasarar kama mutum uku daga cikin wadanda suka aikata laifin tare da kwato makaman da suka yi amfani da su, inda tuni aka tsare su domin gudanar da bincike.
Ya kara da cewa rundunar na hada kai da ‘yan sanda domin gano sauran wadanda suka tsere.
An riga an binne gawar marigayin AbduRauf A. Shariff bisa koyarwar addinin Musulunci bayan an kammala binciken likitoci.
An Kama Mutane Uku Kan Kisan Jami’in NSCDC A Kano

