Mutane 6 sun mutu a rikicin wani hatsarin mota akan titin Lagos-Ibadan

Fasinjoji shida aka bada rahoton sun mutu a wani hatsarin mota da ya faru ranar Alhamis akan babban titin Lagos zuwa Ibadan.

Hatsarin da ya rutsa da wata motar Hiace ta fasinja mai cin mutane 18 da kuma wata babbar mota ya faru ne a wajejen NASFAT dake babban hanyar.

Hotuna da kuma fefan bidiyo da aka dauka a wurin da abun ya faru ya nuna fasinjoji a kwance a gefen titi basa cikin bayyacinsu a yayin da mutane dake wucewa suka taru domin kai musu É—auki.

Wasu da suka sheda faruwar hatsarin sun ce motar  fasinjar dake fitowa daga Lagos ta ci karo da babbar motar a dai-dai lokacin da take kokarin juyawa ta koma daya hannun titin.

Hukumar kiyaye afkuwar haÉ—ura ta tarayya FRSC reshen jihar Ogun ta tabbatar da faruwar hatsarin.

Odunsi Alabi jami’in wayar da kan jama’a na hukumar FRSC a jihar Ogun ya ce fasinjoji 8 hatsarin ya rutsa da su inda 6 daga ciki suka mutu a yayin da guda biyu ke asibiti suna samun kulawar likitoci.

More from this stream

Recomended