Yan sanda sun kashe dan fashi da makami a Nasarawa

Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Nasarawa ta ce an kashe wani da ake zargin dan fashi da makami a lokacin da jami’an rundunar ke aikin sintiri akan titin Lafia-Obi dake jihar.

A wata sanarwa ranar Asabar, Rahman Nansel mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 07:45 na daren ranar

Nansel ya ce lamarin ya faru ne lokacin da jami’an rundunar da suka fito daga ofishin yan sanda na Jenkwe da suke tsaka da aikin sintiri suka yi arangama da wasu yan fashi su biyar da suka tsare kan babban titin.

Wanda ake zargin sun bude wuta kan tawagr jami’an yan sandan bayan da suka hange su.

” A yayin da ake musayar wuta an kashe daya daga cikin mutanen da ake zargin yan fashi ne a yayin da sauran suka tsere cikin daji da raunukan harbin bindiga,”

“An samu wata karamar bindiga kirar gida da kuma harsashi daga wanda aka kashe,”

More from this stream

Recomended