
Akalla mutane 9 aka bada rahoton sun mutu a ranar Asabar bayan da wasu abubuwa biyu da ake zargi bama-bamai ne sun fashe akan hanyar Magami-Dansadau dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Ana zargin yan fashin daji ne su ka dasa bama-baman akan hanyar a tsakanin garuruwan Maikogo da Maiayaya.
Bom na farko da ya tashi ya lalata wasu babura biyu tare da kashe mutane hudu a yayin da fashewa ta biyu ya rutsa da wata motar tirela inda mutane biyar suka mutu.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito cewa wata mata ta fado daga kan wata mota lokacin da aka shiga rudanin fashewar bam din inda wata mota tabi ta kanta ta mutu nan take.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar ya ce kawo yanzu rundunar bata tattara cikakkun bayanai ba kan harin.

