NSCDC Ta Tura Jami’ai 1,100 A Fadin Bauchi Don Tabbatar Da Tsaro A Lokacin Kirsimeti Da Sabuwar Shekara

Hukumar tsaron farar hula ta Najeriya (NSCDC) ta tura jami’anta sama da 1,100 a fadin Jihar Bauchi domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma yayin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

Kakakin hukumar a jihar, Saminu Yusuf, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata. Ya ce an shirya wannan mataki ne domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duk tsawon lokacin bukukuwan karshen shekara.

A cewarsa, jami’an za su yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro ta hanyar gudanar da sintiri na hadin gwiwa a wuraren da ake ganin na iya fuskantar barazana, tare da tsaron muhimman kadarorin gwamnati da ababen more rayuwa. Haka kuma za a tabbatar da tsaro a wuraren ibada, tashoshin mota, gidajen abinci, bankuna da otel-otel.

Sanarwar ta kara da cewa Kwamandan NSCDC na jihar, Oloyede Nelson Oyerinde, ya gargadi jami’an da su kasance masu jajircewa, gaskiya da kwazo wajen gudanar da ayyukansu. Ya kuma umurce su da su kara yawan sintiri, su rika mamaye wuraren taruwar jama’a, tare da kasancewa masu lura da duk wani abu da ka iya barazana ga tsaro kafin, lokacin da kuma bayan bukukuwan.

Oyerinde ya shawarci mazauna jihar Bauchi da su guji duk wani abu da ka iya tayar da hankalin jama’a, tare da bukatar su rika kai rahoton duk wani abu da suka ga yana da alamar hatsari zuwa ofishin NSCDC mafi kusa da su.

Hukumar ta kuma taya jami’anta da mazauna jihar murnar Kirsimeti da Sabuwar Shekara, tare da tabbatar wa jama’a cewa an tanadi isasshen tsaro domin ganin an yi bukukuwan cikin kwanciyar hankali da walwala.

More from this stream

Recomended