Hukumar PSC Ta Buɗe Shafin Daukar ‘Yan Sanda 50,000 A Fadin Najeriya

Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda ta Ƙasa (PSC) ta sanar da fara daukar sababbin ‘yan sanda 50,000 a fadin Najeriya, a wani mataki na ƙarfafa aikin tsaron al’umma da inganta tsaro a cikin gida.

Sanarwar ta fito ne a ranar Litinin, inda Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Sokoto ta bayyana cewa an buɗe shafin neman aikin a yau, 15 ga Disamba, 2025. Wannan na zuwa ne bisa umarnin Shugaban Ƙasa, domin ƙara yawan jami’an rundunar.

Hukumar ta jaddada cewa aikin daukar ‘yan sandan kyauta ne gaba ɗaya, tare da gargadin jama’a da su guji masu neman kudi ko wasu shafuka marasa izini.

A cewar sanarwar, masu nema dole ne su kasance ‘yan ƙasar Najeriya ta haihuwa, su mallaki lambar shaidar ƙasa (NIN), sannan su kasance lafiyayyu ta fuskar jiki, hankali da lafiya gaba ɗaya.

Sanarwar ta ce: “Dole ne masu nema su kasance ba su da tarihin aikata laifi ko matsalar kudi, kuma su cika dukkan sharuddan da aka tanada a shafin daukar aikin na hukuma.”

An bayyana cewa aikin daukar ya kasu kashi biyu: na General Duty da na Specialists. Ga bangaren General Duty, dole ne masu nema su kasance tsakanin shekaru 18 zuwa 25, su mallaki aƙalla kiredit a darussa biyar na WAEC, SSCE ko NECO (ba a fiye da zama biyu ba), ciki har da Turanci da Lissafi. Haka kuma, tsayin namiji ya kasance aƙalla mita 1.67, yayin da mace ke bukatar mita 1.64.

Game da bangaren Specialists kuwa, masu nema su kasance tsakanin shekaru 18 zuwa 28, su mallaki aƙalla kiredit a darussa huɗu da suka dace, tare da takardun shaidar ƙwarewa ko sana’a da kuma aƙalla shekaru uku na gogewa a fannoni kamar lafiya, fasahar sadarwa (ICT), injiniya, tukin mota da gyaran ababen hawa.

PSC ta sanar da cewa shafin neman aikin zai kasance a buɗe na tsawon makonni shida, kuma zai rufe da misalin ƙarfe 11:59 na dare ranar Lahadi, 25 ga Janairu, 2026. An bukaci masu sha’awa da su nema ta hanyar shafin hukuma kaɗai: npfapplication.psc.gov.ng, inda aka yi gargadin cewa neman aiki fiye da sau ɗaya ko yunƙurin yin tasiri zai kai ga gaggawar zirɗe mutum.

More from this stream

Recomended