An gabatar da sabbin sojojin Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya a wani bikin yayewa da aka gudanar a yau Asabar a birnin Zaria, bayan kammala horo na tsawon watanni shida.
Hafsan Sojojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, wanda ya halarci bikin, ya yaba wa sabbin sojojin kan jajircewarsu, tare da buƙatar su dage wajen kare ƴan ƙasa da mutunta ƙa’idojin aikin soja.
An Yaye Sabbin Sojoji 3,439 Bayan Horo Na Wata Shida A Zaria

