
Mambobin majalisar dokokin jihar Zamfara biyu yan jam’iyar APC sun sanar da ficewa daga jam’iyar inda suka alakanta hakan da rarrabuwar kai a cikin jam’iyar da kuma zargin rashin adalci daga shugabanninta.
Mai tsawatarwa marasa rinjaye, Hon Nura Dahiru Sabon Birnin Dan Ali dake wakiltar al’ummar Birnin Magaji a zauren majalisar ya sanar da fitarsa daga jam’iyar a wata wasika da ya aikewa da shugaban APC na jihar, Tukur Danfulani.
A cikin wasikar ya bayyana cewa ya dauki matakin ne biyo bayan tattaunawar da ya yi al’ummar da yake wakilta da kuma abokanan tafiyarsa a siyasance.
Har ila yau shima Hon Shamsuddeen Hassan Basko wanda ke wakiltar mazabar Talata Mafara North ya sanar da fitarsa daga jam’iyar ta APC.
A wasikar fita daga jam’iyar Hassan ya ce ya fice daga jam’iyar ne bayan da ya yi waiwaye na tsanaki kan rikicin cikin gida, rabe-rabe da kuma yadda aka mayar da wasu saniyar ware a jam’iyar a matakin Æ™ananan hukumomi da jiha.

