Yarjejeniyar Zaman Lafiya Ta Fara Haifar da Ɗa Mai Ido a Katsina — Gwamna Radda

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa yarjejeniyar zaman lafiya da al’ummomi suka kulla da ’yan bindiga a wasu yankuna na jihar suna fara nuna tasiri, inda ake samun raguwar hare-hare da sace-sacen mutane.

Radda ya yi wannan bayani ne yayin ziyararsa a kananan hukumomin Batsari da Danmusa, a ci gaba da rangadin da yake yi a fadin jihar domin duba matsalolin tsaro da ci gaban al’umma.

A cewar gwamnan, wasu al’ummomi da suka dade suna fama da hare-hare sun cimma sulhu da kungiyoyin ’yan bindiga, lamarin da ya taimaka wajen rage kashe-kashe da garkuwa da mutane. A matsayin nuna ci gaban da ake samu, gwamnan ya ziyarci dajin Danburum da ke Batsari — wani yanki da jama’a ke guje wa wucewa saboda barazanar ’yan bindiga.

Ya ce a kwanakin baya-bayan nan gwamnati ba ta samu rahotannin munanan hare-hare daga hukumomin tsaro ba. “Shirin zaman lafiya da al’ummomi suka jagoranta yana haifar da sakamako. A cikin kwanaki da dama, ban samu ko rahoton hari daya daga jami’an tsaro ba,” in ji shi.

Radda ya kara da cewa kudaden da gwamnati ke kashewa wajen kula da wadanda hare-haren ’yan bindiga suka rutsa da su sun ragu kwarai. Hukumar jin kai ta jihar da ke kashe sama da Naira miliyan 40 a wata, ta kashe kasa da Naira miliyan 2 a watan Nuwamba.

Sai dai ya jaddada cewa duk da raguwar hare-hare, ba a kawar da matsalar ’yan bindiga gaba daya ba. Gwamnan ya bukaci jama’a da shugabannin addini su kara dagewa da addu’o’i domin dorewar zaman lafiya a jihar.

More from this stream

Recomended