Wike Ya Ce Har Yanzu Shi Dan Jam’iyyar PDP Ne, Ya Karyata Korar da Turaki Ya Yi Masa

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana a ranar Juma’a cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), duk da sanarwar da wani ɓarin jam’iyyar da ke goyon bayan shugaban jam’iyyar na kasa, Kabiru Turaki, ya fitar cewa an kori wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar har 11 ciki har da shi.

Turaki ya tura takardun korar ga wasu fitattun ’yan jam’iyyar, ciki har da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, Sanata Samuel Anyanwu, Umaru Bature, Kamarudeen Ajibade (SAN), Abdurahman Muhammad da Sanata Mao Ohuabunwa, yana mai cewa matakin na da nufin tsaftace jam’iyyar kafin zaben 2027.

Da yake mayar da martani bayan ya kammala duba gadar da ke hada titin da ke hada Gwarinpa da Jahi, wanda ke kai tsaye zuwa Katampe, Gishiri da Maitama, Wike ya ce ikirarin korar ba gaskiya ba ne, yana mai cewa zai ci gaba da aiki tare da sauran ’yan jam’iyyar wajen tabbatar da cewa PDP ta ci gaba da taka rawar gani a matsayin jam’iyyar adawa.

Ya ce, “Wadanda suka raba kan jam’iyyar su ne za su bar ta. Ni har yanzu ina PDP, kuma kamar yadda kuke gani, ba kowa ya fita ba. Muna da mutane masu yawa kuma za mu ci gaba da aiki tare. Na sha fada wa jam’iyya ta gyara gidanta, domin idan ba ta yi hakan ba, ita ce abin zai shafa.”

Wike ya kara da cewa akwai bukatar a yi aiki tare domin tabbatar da cewa PDP ta kasance jam’iyyar adawa mai karfi a kasar.

More from this stream

Recomended