Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta cafke wani da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi, Ogbu Simon, a ƙaramar hukumar Ningi, inda ta kuma kwato ƙwayoyi masu yawa da ƙimar su ta kai kusan naira miliyan 12.2.
Cikin bayanin da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, CSP Mohammed Wakil, ya fitar, an ce kama mutumin ne biyo bayan bayanan sirri daga wani game da abin da ake zargi yana faruwa a shagon Simon, wanda ake zargin yana kawo ƙwayoyi daga Onitsha, Jihar Anambra, zuwa Ningi da kewaye.
A yayin samamen da aka gudanar a ranar 26 ga Nuwamba, tawagar DPO na Ningi, CSP Surajo Ibrahim Birnin Kudu, ta gano sachet 17,500 na Tramadol da kuma fakiti 487 na Diazepam (D5), da ake kira “Yellow Voice.”
Daga bisani, tawagar Operation Restore Peace (ORP) ƙarƙashin jagorancin CSP Abdulrazak Fada ta kama wanda ake zargi, inda ya amsa cewa yana rarraba miyagun ƙwayoyin zuwa kasuwanni da dama a ciki da wajen Ningi.
An ce za a miƙa ƙwayoyin tare da wanda ake zargi ga hukumar NDLEA reshen Bauchi domin cigaba da bincike da gurfanarwa.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Sani Omolori Aliyu, ya tabbatar da kudirin rundunar na ci gaba da yaki da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba da hadin kai don dakile laifuka a jihar.
‘Yan Sanda a Bauchi Sun Kama Wani Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Tare da Ƙwace Ƙwayoyi Na Miliyoyin Naira

