Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya mika sunan tsohon Shugaban Ma’aikatan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (ritaya), domin nada shi sabon Ministan Tsaro.
Tinubu ya bayyana sunan Musa a cikin wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, yana mai cewa zai maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru, wanda ya yi murabus a ranar Litinin.
Janar Musa ya jagoranci rundunar tsaro ta ƙasa daga 2023 zuwa Oktoba 2025, kuma ya taɓa lashe lambar yabo ta Colin Powell Award for Soldiering a 2012.
An haifi Musa a Sokoto a 1967, inda ya yi makarantar firamare da sakandare, kafin ya tafi College of Advanced Studies da ke Zariya. Ya kammala karatunsa a 1986 sannan ya shiga Nigerian Defence Academy (NDA) a shekarar da ya gama. Ya samu digirin Bachelor of Science a 1991.
Tinubu Ya Naɗa Tsohon Babban Hafsan Tsaro Janar Christopher Musa a Matsayin Ministan Tsaro

