Ƴanbindiga Sun Hallaka Jami’an ‘Yan Sanda Guda 5 a Bauchi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da rasuwar jami’anta biyar sakamakon wani kwanton ɓauna da ‘yanbindiga suka kai musu.

A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Ahmad Wakil, ya fitar, jami’an suna kan aikin wanzar da zaman lafiya ne tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Sabon Sara da ke karamar hukumar Darazo, kafin a farmake su.

Sanarwar ta ce yayin harin, wasu jami’an guda biyu sun samu raunuka sosai, sai dai dakarun sun yi nasarar kashe wasu daga cikin ‘yanbindigar da suka kai harin.

Ya ce: “Abin baƙin ciki, kwanton ɓaunar ya yi sanadiyyar mutuwar jami’ai kamar haka: DSP Ahmad Muhammad (SID), ASP Mustapha Muhammad (10 PMF), Sufeto Amarhel Yunusa (10 PMF), Sufeto Idris Ahmed (10 PMF), Kofur Isah Muazu (AKU).”

Rundunar ta ce tana ci gaba da jajantawa iyalan mamatan da kuma tabbatar da cewa za ta dauki matakan da suka dace domin ganin an kawo karshen masu aikata laifukan tashin hankali a yankin.

More from this stream

Recomended